Sakamakon halayyar kirki da karramawa da martaba malam Bahaushe a idon duniya, Masarautar taga dacewar karrama Auwalu mai Adaidaita daya tsinci kudi Milyan 15, tare da gidan radiyon Arewa da suka sanar da cigiyar.
A ranar asabar ne mai martaba Dr Abdulkadir Koguna sarkin Hausawan Afirka kuma Sardaunan Agadas ya bawa Auwalu salisu Ambasadan Hausawan Afirka.
Baya ga haka masarautar ta naɗa shi Ɗan Amanar Hausawan Afirika, wanda a karshen shekarar nan za a yi bikin nadin
Haka kuma masautar ta karrama Arewa Radio bisa wannan kokarin da suka yi suma.
Mai Martaba ya kara kira matasa da suyi riko da gaskiya da amana a dukkan lamuransu, kuma suyi koyi da Auwalu, domin ya nuna akwai na Allah a cikin masu sana’arsu ta adaidaita Sahu.



Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo