Hatsarin Mota Ya Hallaka Jami’an Ƴan Sanda Uku

Alfijr ta rawaito Wasu ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Ƴan sandan na tafiya ne zuwa karamar hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Dauche a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya afku da misalin karfe 9 na dare.

An ruwaito cewa ɗaya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ne ya fashe a kauyen Sako, a Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.

Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.

Hotuna da aka gani, sun nuna jami’an jina-jina, inda wasu suka samu munanan raunuka a kawunansu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

One Reply to “Hatsarin Mota Ya Hallaka Jami’an Ƴan Sanda Uku”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *