Handama Gwamnatin jigawa ta dakatar da kwamishina a jihar

FB IMG 1712351450735

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya dakatar da kwamishinan kasuwanci na jihar, Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin karkatar da wasu kudade da aka ware domin ciyar da ciyar da azumin watan Ramadan a karamar hukumar Babura ta jihar.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take har sai an sake nazari nazari wanda kwamitin binciken da gwamnan jihar ya kafa kan zargin.

A cewar sanarwar, matakin da gwamnan jihar ya dauka na daga cikin kokarinsa na tabbatar da bin doka da oda da kuma tafiyar da kudaden gwamnati cikin tsanaki.

Idan dai za a iya tunawa majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da Naira biliyan 2.8 don ciyar da azumin watan Ramadan a fadin kananan hukumomin jihar 27.

A karkashin shirin, an samar da cibiyoyi 600 da mafi karancin maki biyu a kowace unguwa da kuma wasu cibiyoyi da aka kebe a kowace manyan cibiyoyi da ke jihar, yayin da ake ciyar da a kalla mutane 300 a kowace rana a kowacce cibiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *