Gwamnatin Najeriya Tayi Umarnin Fara Sayar Da Buhun Shinkafa N40,000 A Fadin Kasar

FB IMG 1722327197513

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta fara raba manyan motocin shinkafa goma-goma ga kowace jiha, domin sayar da kowane buhu mai nauyin kilo giram 50 a kan farashin N40,000.

Alfijir labarai ta ruwaito majalisar Zartarwar ta FEC ta ce babu buƙatar zanga-zangar tsadar rayuwa, ta na mai cewa ana ƙoƙarin magance mafi yawancin matsalolin da masu shirya ta su ka zayyano a zaman majalisar ranarLitinin da ta gabata.

Yayin da ake kusantar lokacin zanga-zangar, Shugaba Tinubu ya ce, ya na ƙoƙarin magance matsalolin matasan.

Ministan labaru, Mohammed Idris ya ce raba shinkafar wani ɓangare ne na ƙoƙarin magance matsalolin talauci da tsadar rayuwa. Ya kara da cewar hakan ɗaya ne daga cikin abubuwa da dama da gwamnati ke yi wajen tallafa wa ƴan Nijeriya.

Ya ƙara da nuni da ƙoƙarin gwamnati na samar da tsare-tsaren bayar da aron kuɗin karatu ga ɗalibai da shirye-shiryen ɗaukar aiki, da sanya hannayen jari a harkokin noma waɗanda su na cikin buƙatun ƴan zanga-zangar.

Bugu da ƙari, ya yi kira ga ƴan zanga-zangar da su sake nazari, ya na mai cewa hakan kan iya juyawa zuwa tashin-tashina a cikin al’umma inda ya ce su ƙara haƙuri yayin da gwamnati ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin ƙasa baki ɗaya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *