Gwamnatin Najeriya Ta Sake Ayyana Hutun Ranar ’Yancin Kan Ƙasar

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu don bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun yancin kai.

Alfijir Labarai ta rawaito Olubunmi Tunji-Ojo, a wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida ya fitar a ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a madadin gwamnatin tarayya, ya ayyana Litinin, 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu.

A cikin sanarwar tasa, ministan ya taya ‘yan Najeriya na gida da waje murnar samun ‘yancin kai.

A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Oluwatoyin Akinlade, ministan ya bayyana jajaircewar gwamnatin tarayya na tunkarar kalubalen da ke addabar kasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *