Gwamnatin Najeriya ta ce za ta hukunta likitocin dake da hannu a safarar Koda

IMG 20231221 122230

Gwamnatin Najeriya ta bayar da tabbacin ɗaukan mataki kan likitoci da sauran mutanen da ke da hannu a harkar safarar ƙoda.

Alfijir labarai ta rawaito Jami’ar yaɗa labarai ta ma’aikatar lafiya ta ƙasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba a Abuja, babban birnin Najeriya.

A cewar jami’ar, gwamnati ta sanar da ƙudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar ƙoda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a ɓoye.

Ta ce “ma’aikatar ta yi tir da irin wannan mummunar ɗabi’a ta safarar ƙoda kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.

Ma’aikatar lafiyar ta kuma tunatar da mutane game da sashe na 51 zuwa 56 na dokar lafiya ta ƙasa da ya haramta safarar ƙodar.

“Mutanen da suka ƙi bin dokar sun aikata laifi kuma za su iya fuskantar biyan tarar naira miliyan ɗaya ko zama gidan yari ko ma duka biyun.

Ms Patricia Deworitshe ta ce hukumar kula da aikin likitoci ta Najeriya tana duba zarge-zargen da aka yi kan likitoci da suke wannan ta’adar.

Deworitshe ta ƙara da cewa kamata ya yi bayar da gudummawar ƙoda ya zama bisa masaniyar wanda zai ba da ƙodar tasa, kuma bisa shawarar likita.

Fassarar Idongari

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *