Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta sauke shugaban asibitin yara na Hasiya Bayero bisa zargin rashin iya shugabanci.
Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa dauke da sahannun jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman, ta ce an dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Yusuf Labaran da shugaban hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda.
Sanarwar ta zargi shugaban asibitin na Hasiya Bayero da aka sauke da gazawa wajen tsara ma’aikata tare da aiwatar da manufofin gwamnati da aka ayyana na duba marasa lafiya da kuma kula da su kyauta.
Hakazalika Dr. Nagoda na korafin cewa shugaban ya gaza sarrafa ma’aikatansa domin samar da kulawa yadda ya kamata.
An sanar da Dr. Ibrahim Ibn Muhammad a matsayin sabon shugaban asibitin na Hasiya Bayero.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM