Gwamnatin Kano ta sake haɗa wani gangamin taro da wasu kungiyoyi domin magance matsalar kwacen waya da tsaro a jihar

IMG 150035 14725 1752501663148

Ya kamata a karawa masu unguwanni karfi da daraja a aikinsu, duba da su suka san kowa da yake zaune a unguwarsu, wannan zai saurin kawo ƙarshen wannan aika aika.

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishinan yaɗa labarai da ayyukan cikin gida ta sake haɗa wani gangamin taro da wasu kungiyoyi domin magance matsalar kwacen waya da sauran matsalolin tsaro a fadin jihar

Da yake bayanin makasudin taron ga manema labarai Kwamishinan yaɗa labarai da ayyukan cikin gida na jihar Cormarade Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce an haɗa wannan taron ne domin a tattauna matsalolin da ake ciki da shawarwarin da za a bayar domin magance matsalar kwacen waya da ayyukan daba.

Waiya ya kara da cewar wannan matsala ta damu mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf, duk da idan ka kula zaka ga abin yana da nasaba da shaye-shaye da daba, shi yasa ya lashi takobin magance matsalolin a jihar Kano.

Mun san wannani al’amari ya samo asali ne daga daba ta unguwanni da kuma ta siyasa kamar yadda gwamnatocin baya suka assasa, musamman gwamnatin data wuce domin biyan buƙatunsu. In ji Waiya.

Duk da dadewar wannan lalatar, mai girma Gwamna ya kudiri aniyar kawar da ita cikin taimakon Allah.

Don haka duk wasu kungiyoyi masu zaman kansu a fadin wannan jihar da muka san suna nuna damuwarsu, sannan kuma suna maganganu akan lamarin, muka gayyato su domin mu tattauna dasu mu sami matsa daya.

A wannan gaɓar nake muku albashir da amincewar gwamna Abba Kabir akan wannan aiki, kuma ya samar da wani kwamiti mai karfi tare da kwararrun mutane domin tunkarar lamarin ba sani ba sabo.

Idan zaku iya tunawa a kwanakin baya, Gwamna ya fito da wani shiri mai suna (Safe Corridor) wato tudun mun tsira, wanda wasu daga cikin matasan dake wannan dabi’ar suka nuna basu da sha aware wannan aika aikar, domin yawancinsu sun ce tursasu aka yi suyi, wasu kuma sun ce jan su aka yi amma suna neman hanyar bari domin bai dace da rayuwar su.

Yanzu haka shiri yayi nisa, yanzu haka ana tattara wadannan matasan domin a nemar musu abin yi, tare da haɗin guiwar shugabannin ƙananan hukumomi musamman na cikin birnin domin kawo karshen al’amarin da izinin Allah.

Da yawa daga cikin maharta taron sun tofa albarkacin bakinsu akan hanyoyin da ya kamata gwamnati ta bi domin kawo karshen wannan iyashege.

Haj Rakiya na daga cikin shugabannin kungiyoyin ta bada shawara mai mahimmancin gaske, inda take kira da gwamnatin cewar, ya kamata a karawa masu unguwanni karfi da daraja a aikinsu, duba da su suka san kowa da yake zaune a unguwarsu, wannan zai saurin kawo ƙarshen wannan aika aika.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *