Kan haka ne na amince da a dauki karin malaman makaranta aikin dindindin
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya aminta da mayar da dukkanin Ma’aikatan wucin gadi na S-power dake aiki a makarantun firamare da sakandaren jihar Katsina a matsayin Ma’aikatan dindindin a duk fadin jihar

Cikin wani bayani da Gwamna Radda ya wallafa a shafinsa na facebook yace “Bisa tsarin da na ke da shi na inganta rayuwar matasan da ke tasowa, da kuma azamar da nake da ita ta inganta ilmi ta hanyar kara yawan malaman makaranta a jihar Katsina”.
Kan haka ne na amince da a dauki karin malaman makaranta aikin dindindin su 7,325 da suke aikin wucin-gadi da wadanda suke a cikin shirin S-POWER da suka yi nasarar cin jarabawar da aka shirya musu don zabo hazikai kuma nagartattun malaman makaranta daga cikin 7,673 da suka zauna jarabawar gwajin inganci.
Hakika an dade ba a dauki malaman makaranta masu yawan haka ba a tarihin jihar Katsina. In ji Gwamnan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb