Gwamnan Kano Ya Sake Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Mukami

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada Malam Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin Kwamanda hukumar Hisba ta jiha.

Alfijir Labarai ta rawaito Sheikh Aminu Daurawa shine tsohon camandan hukumar lokacin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Kuma lokacin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a farko farko.

Sheikh Daurawa dai ya bar kujerar Kwamandan hukumar Hisbah ne bayan samun sabini na siyasa tsakaninsu da tsohon gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne ya gudanar da tsarin auren zawarawa a hukumar lokacin da ya riƙe muƙamin a karon farko zamanin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

2 Replies to “Gwamnan Kano Ya Sake Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Mukami

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *