
Alfijr ta rawaito Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf da sanyin safiyar Asabar ya kaddamar da fara rusa shaguna da gidajen da jama’a suka yi i ba bisa ka’ida ba.
Rahotanni sun nuna cewa wani gini mai hawa uku mai shaguna 90 a kan titin fiilin Sukuwa, an tuguje shi da misalin karfe 2:00 na ranar Asabar.
Gwamnan wanda ya jagoranci aikin rusa ginin ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sanda, Muhammed Gumel.

Idan dai za a iya tunawa Abba Kabir Yusuf bayan zaben sa, a matsayin zababben gwamnan jihar ya yi barazanar ruguza gine-gine a jihar kan kadarorin jama’a da akayi ba bisa ka’ida ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ