Alfijir Labarai ta rawaito a bisa kudirin gwamnatin jihar Kano na aiwatar da alkawurran da ta dauka a yakin neman zabe da kuma aiwatar da bangaren ilimi na tsarin sa, Gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da shirin.
Sakataren gwamnatin jihar zai fara gudanar da aikin bayar da tallafin karatu na kasashen waje ga ’yan asalin jihar Kano da suka kammala karatun digiri na farko.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2015 ne gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta bayar da tallafin karatu na karshe wanda ya dauki nauyin kashi na uku na aji 503. karatu zuwa kasashe 14 daban-daban na duniya.
Dangane da ci gaban, ana gayyatar waɗanda suka cancanta don samun digiri na biyu na waje da na cikin gida na jihar Kano na shekara ta 2023/2024.
Duk wanda ya cancanci samun tallafin karatu dole ne ya zama ɗan asalin jihar Kano mai digiri na farko ko makamancinsa daga jami’a ko cibiyoyi masu daraja, Ɗaliban su kasance lafiyayyu kuma.
Ɗalibai da suka cika sharuddan da aka bayyana a sama za su iya shiga yanar gizo,
www.kanostategov.ng./scholarship
Bayan kammala wannna kuma, za a gayyace su don tantance su a ofishin sakataren gwamnatin jihar.
Yayin wannan Atisayen kuma Ɗalibai za su zo da kwafin takardun shaidar karatu wanda ya kunshi; takardar shaidar dan kasa, takardar shaidar likita, takardar shaidar haihuwa, takardar shaidar makarantar firamare, takardar shaidar WASC/GCE/SSCE, takardar shaidar digiri.
Wannan atisayen zai dauki kwanaki sha hudu (14) daga yau.

Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano ya sanyawa hannu
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Think you
Thanks