Wannan mafari ne, saboda za a fara aiwatar da wasu manyan tsare-tsare nan ba da jimawa ba,
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da rabon shinkafa domin rage radadin tallafin man fetur ga ƴan kasa.
An kaddamar da rabon kayayyakin Tallafin ne a ranar Asabar a sakatariyar karamar hukumar garin Dutse.
Wani bincike ya tabbatar da gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar kudi sama da N134m domin siyan tireloli na shinkafa guda biyar domin rage tasirin cire raɗaɗin tallafin man fetur.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan ya ce rabon shinkafar wani bangare ne na matakan da gwamnati ta dauka domin rage raɗaɗin.
“Kayan tallafin sun hada da buhunan shinkafa, da kuma tsabar kudi na nau’ukan masu kananan sana’o’i da za a zabo daga dukkan unguwanni da ke fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
“Wannan mafari ne, saboda za a fara aiwatar da wasu manyan tsare-tsare nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Don haka ya roki jama’a da su yi hakuri da halin kuncin da kasar nan ke ciki, yana mai bayyana hakan a matsayin wani lamari na duniya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM