Gwamna Abba Kabir da Gwamna Bala Tare da Gwamna Lawan sun isa Kotun ƙoli

FB IMG 1705050786363

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya isa harabar Kotun ƙoli da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ya ɗaukaka don ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta soke nasararsa.

Gwamna Abba Kabir yana ƙalubalantar hukuncin ne bayan da ƙananan hotuna suka bai wa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna nasara.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri’a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam’iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

FB IMG 1705050587471
Sanusi Bature/Facebook

Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo (Hagu)Image caption: Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo (Hagu)

FB IMG 1705050783224
Sanusi Bature/Facebook

Shi ma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na jamiyyar PDP ya isa kotun ƙolin bayan da ɗan takarar Jam’iyyar APC a zaben da aka yi bara, Saddique Abubakar ya shigar da ƙarar ƙalubalantar nasarar gwamnan.

FB IMG 1705050789298
Sanusi Bature/Facebook

Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.

Saddiqu Abubakar dai ya yi iƙirarin cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri’ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.

Gwamna Lawali zamfara da Gwamnan kano

FB IMG 1705050786363
Sanusi Bature/Facebook
FB IMG 1705050792327
Sanusi Bature/Facebook

Hakazalika an tsaurara matakan tsaro a dukkan hanyoyin da za su kai ga kotun ƙoli da ke sauraron shari’oin zaɓukan gwamna da aka ɗaukaka daga faɗin ƙasar.

Jihohin su ne Kano da Legas da Filato da Bauchi da Ebonyi da Zamfara da Cross River.

Shari’oin zaɓen gwamnan Kano d Filato na daga cikin waɗanda hankali ya karkata a kan su kasancewar su ne waɗanda ƙananan kotuna suka rushe zaɓen gwamnonin da ke ci.

A cewar bayanai, jami’an tsaro sun hana ƴan jarida da lauyoyi da ƴan siyasa da ba su da shaidar shiga harabar kotun.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *