Gobarar Man Fetur Ta Hallaka Mutum 34 Wasu 20 Sun Jikkata

A kalla mutum 34 sun rasa rayukansu yayin da aka samu tashin wutar gobara a wani wajen ma’ajiyar Mai a Jamhuriyyar Benin yayin da wasu mutum 20 kuma suka samu munanan raunuka.

An ce, wutar ta tashi ne a wata haramtacciyar ma’ajiyar mai da ke Semi-Podji – wani garin da ke kan iyaka da Nijeriya.

Ministan kula da harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin, Alassane Seidou, ya shaida wa ‘yan jarida cewa, jarirai biyu na daga cikin wadanda suka mutu.

“Abun bakin ciki mutum 34 ciki har da jarirai biyu sun mutu. Gangar jikinsu ya kone sakamakon tashin wutar gobarar mai,” Seidou ya shaida.

Ya kara da cewa, a halin da ake ciki wadanda suka jikkata kuma suna kan amsar kulawar likitoci a asibiti.

Duk da cewar ministan bai bada wani karin haske kan masu safaran mai din ba, ana dai yawan samun safaran mai daga Nijeriya zuwa jamhuriyyar Benin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *