Gobara Tayi Sanadin Mutuwar Uwa da Ƴaƴanta Ta Biyu A Jigawa


Alfijr ta rawaito wata uwa mai suna Khadija Ibrahim ‘yar shekara 30 da ‘ya’yanta mata biyu sun mutu a wata gobara da ta tashi a kauyen Tsangarwa da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, Command CSC Adamu Shehu, ya bayyana faruwar lamarin a ranar Juma’a, da misalin karfe 11:00 na safe, inda gobara ta kone wata bukka a lokacin da wadanda abin ya shafa ke shirgar barci.

Sanarwar ta ce “Hatsarin gobarar ta lakume wata bukka da wata yarinya Khadija Ibrahim ‘yar shekara 30 ke kwana tare da ‘ya’yanta mata guda biyu, Aisha Ibrahim ‘yar shekara 4 da kuma Rabi Ibrahim ‘yar shekara 2.

Ya bayyana cewa duk da mahaifiyar da ‘ya’yanta mata guda biyu gobarar ta cinye gaba daya saboda babu daya daga cikin wadanda abin ya shafa da aka ceto da ransu.

‘’CSC Adamu ya ce ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma makwabta sun ce watakila ba za a rasa nasaba da wutar gawayi da ake son sanya musu dumi ba,’’ in ji sanarwar.

Jami an sun garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su asibiti, likitoci sun tabbatar da mutuwar su bayan cikakken bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *