Gidauniyar Zaks foundation ta saukewa ɗaliban wasu makarantu kabakin arziki

IMG 20231128 WA0000
Pinterest Hidden Image

Gidauniyar Zaks Foundation for Humanity (ZFH), wata kungiya mai zaman kanta da ke Abuja, wadda ke bi makarantu domin tallafa musu wajen magance matsalolin da ke addabar dalibai da kayan koyo dana koyarwa.

Hakazalika kungiyar na maida hankali wajen gudanar bada tallafi ne, musamman a ɓangaren abinda ya shafi rayuwar ƴaƴa mata wajen tsaftace rayuwarsu.

A wannan karon daya daga cikin shiryin da kungiyar ta gudanar ga ɗalibai mata a jihar Neja ne, a wasu makarantu kamar haka:-

Government Girls Secondary School Bakin Uku.

Makarantar Sakandaren Gwamnati Katonme Suleja.

Sun rabawa ɗalibai mata audugar bakon wata-wata ne (Jinin Haila) domin tsaftace kansu, duba da irin halin kuncin rayuwa da ake ciki na tsadar rayuwa.

Sun gudanar da wannan tarone a ranar Litinin 27th Nuwamba 2023 da karfe 10 na safe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *