Gargadi: Hukumar CAC Zata Rufe Wasu kamfanoni 100,000 A Najeriya

Hukumar kula da harkokin kasuwanci ta ce za ta rufe kamfanoni 100,000 da suka gaza gabatar da kudaden shiga na shekara.

Alfijir Labarai ta rawaito babban magatakardar hukumar ta CAC, Garba Abubakar, a cikin wata sanarwa da ya fitar, lokacin da yake jawabi a wajen wani taron horaswa kan yadda ake amfani da rajistar mallakar (BOR) a Lagos.

Abubakar, ya ce nan ba da dadewa ba Hukumar za ta aike da sanarwa ga kamfanonin da abin ya shafa kafin fara daukar matakin kamar yadda yake a sashe na 692 na CAMA,2020.

Ya bayyana cewa, duk da haka, kamfanonin suna da damar sake biyan basussukan da ke kan su da kuma umarnin kotu, kamar yadda doka ta tanada.

Don haka Abubakar ya shawarci kamfanoni da su tabbatar da biyan kudaden komawar su a kan kari don gudun kada a hana su.

A kan BOR, ya ce CAC ce ta gina shi tare da tallafi da taimakon bankin duniya.

Babban magatakardar ya jaddada cewa, rijistar za ta taimaka sosai wajen dakile cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram, da samar da kudaden ta’addanci.

Don haka ya umarci masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin bincike, masu shari’a, ‘yan jarida, da kungiyoyin farar hula da su yi amfani da BOR wajen sauke nauyin da ke kansu.

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, bangaren dokar kasuwanci, (NBA-SBL), Dokta Adeyeye Adefulu, ya yabawa hukumar ta CAC da ta sake daukar wani muhimmin mataki a tarihinta.

Don haka Adefulu ya ce NBA-SBL za ta ci gaba da dorewar kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da Hukumar, ya kuma hori mambobin kungiyar da su yi amfani da ilimin da suka samu a wannan horon domin amfanin tattalin arzikin Najeriya.

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan canji ta Najeriya (ABDCON), Aminu Gwadabe, ya jaddada muhimmancin kungiyar ta BOR wajen yaki da safarar kudade da kuma samar kudaden ta’addanci.

Gwadabe, ya shawarci kwararru da su yi taka-tsantsan wajen tunkarar abokan huldar su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *