
Alfijr ta rawaito yadda Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado ya jagoranci kaddamar da sabbin gidajen malaman makaranta guda 500 wanda gwamnatinsa ta gina a karamar hukumar Ungoggo.
Gwamna Ganduje ya jagoranci kaddanar da gidajen tare da shugaban kungiyar yan kwadago ta kasa Commrade Joseph Alero inda akayi musu laqabi da Comrade Kabiru Ado Minjibir Estate.

Haka zalika Gwamnan ya yafewa malaman basussukan da gwamnati ke binsu akan gidajen duk domin a kara inganta rayuwar da inda zasu baiwa al’ummar Kano ilimi cikin yanayi me kyau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ