Alfijr ta rawaito Gamayyar kungiyoyin Malamai da kungiyoyin Musulunci a jihar Kano, ta bayyana hukuncin da wata babbar kotun Shari’a ta yanke hukuncin kisa kan Abduljabbar Nasiru Kabara a matsayin abin farin ciki.
Wata sanarwa da Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa ya sanya wa hannu a madadin kungiyar ta ce, tun daga lokacin da aka fara shari’ar kungiyar ta bi dukkan shari’ar kuma ta gamsu da hukuncin karshe da kotun ta yanke.
Ya kara da cewa an bai wa wanda aka yanke wa hukuncin duk wata dama ta kare kansa a kan dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, da shaidun da aka gabatar, amma ya kasa.
“Wannan hukunci, muna fata, zai zama izna ga sauran wadanda ke da akida iri daya.
“Wannan dandalin, na mika godiya ta musamman ga alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, lauyan masu gabatar da kara da kuma dukkan bangarorin da suka tabbatar da cewa an yi abin da ya dace a shari’ar wanda ake tuhuma da addu’ar Allah ya yi masa jagora.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇