Fusatattun Matasa Sun Kone Kasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane Har Lahira

Hassanat Shehu Kagara

Wasu fusatattun mutane sun yi taho mu gama tare da kone wani Kasurgumin Bahaushe mai Garkuwa da yara a karamar hukumar Lapai ta jihar Neja.

Alfijir Labarai ta rawaito gidan talabijin na LAPAITV ya bayyana wanda ake zargi mai suna Suleiman, ana zarginsa da yunkurin yin garkuwa da wani yaro dan shekara bakwai, lamarin da ya tada zaune tsaye a yankin.

A cewar mahaifin wanda ake zargin, Usman Bamungoro, ya ce wannan mummunan lamari ya faru ne a lokacin da aka aiki ƴaƴansa Abba da Mudasir, suka je siyo kayan marmari a gidan ‘yan uwansu da karfe 9:30 na safe.

Mudasir ya gano dan uwansa a hannun wani mutum motsattse rike da jaka.

Ganin abin ya tsorata, Mudasir ya koma gidan da gudu domin sanar da jama’a da ‘yan uwansa.

Nan take mahaifin Usman tare da gungun mutane suka garzaya wujen neman Abba.

Wanda ake zargi ya tabbatar da cewa yana cikin wasu kungiyoyin masu garkuwa da mutane, wadanda suka hada da mutane goma, ciki har da mata biyu, ya kara da cewa ayyukansu sun fi karkata ne a yankin Lapai.

Lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin mutane dangane da yadda ake yawaita yin garkuwa da mutane a Lapai.

Sakamakon takaici ne wasu fusatattun mutane suka kona wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne har lahira.

Da yake maida jawabi kan lamarin, babban baturen ‘yan sanda (DPO) na Lapai Musa Yusuf, ya ce tuni fusatattun matasan suka kona wanda ake zargin kafin jami’an ‘yan sanda su isa wurin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

One Reply to “Fusatattun Matasa Sun Kone Kasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane Har Lahira”

  1. Allah ya kara tona musu asiri,kuna tare da mutum ashe mugune Allah ya ganar dasu sudaina cutar da al ummar annabi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *