EFCC Ta Karyata Cewar Tana Neman Matawalle Ruwa A Jallo

Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar EFCC ta ce ba ta neman tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ruwa a jallo.

Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter EFCC ta ce ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jan hankalinta da aka yi kan rahoton wata jarida da ta wallafa a ranar Lahadi 18 ga watan Yunin nan da muke ciki da ke cewa tana neman Matawalle ruwa a jallo.

“Hukumar EFCC ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ruwa a jallo ta kuma nemi hukumar tsaro ta fararen kaya DSS ta kama shi “

EFCC ta ce rahoton ba daidai ba ne, ya zuwa yanzu ba ta ayyana Matawalle a matsayin wanda take nema ba, ko neman DSS ta kama mata shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Hukumar na da tsarukanta da take bi ta ayyana mutum a matsayin wanda take nema, kuma tana da hanyoyin da take bi ta sanar da mutane tana neman shi, ba ta hanyar amfani da majiyoyin bogi ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *