Jami’an hukumar shiyyar Kaduna na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da yin sama da fadi da kudaden.
Alfijir labarai ta rawaito wadanda ake zargin: Musa Gideon, Abdul Seidu Adamu da Justine Musa an kama su ne a hanyar Yakubu Gowon, Kaduna a ranar Laraba, 7 ga Fabrairu, 2024 yayin da suke kokarin sayar da sabbin takardun kudi na naira ga wani jami’in hukumar EFCC.
Jami’in, wanda mamba ne na rundunar ta musamman da aka kafa domin aiwatar da wasu dokoki na yaki da cutar da tattalin arzikin kasa da shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi.
Rundunar ta kama mutanen da sayar da jabun sabbin kudi da tsoffi na naira miliyan N1,307,400 (Miliyan Daya Dari Uku da Dubu Bakwai, Naira Dari Hudu) da kuma Mashinan ATM da yawa.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V