EFCC Ta Damke Wani Malamin Addini Da Wasu Tarin Ƴan Yahoo


Alfijr ta rawaito Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun yi babban kamu a birni Ilorin na jihar Kwara a ranar Alhamis, inda suka samu nasarar cafke wasu mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan damfarar yanar gizo wato Yahoo-Yahoo.

Sumamen ya faru ne a unguwar Mandate, cikin birnin Ilorin, biyo bayan samun bayanan sirri da Jami an suka yi kan ayyukan ƴan damfarar da suke aikatawa a unguwar.

Binciken farko da aka gudanar ya bayyana cewa daga cikin ɓata garin da aka cafke akwai wasu malamai da ɗalibai shida na makarantar gaba da sakandire daban-daban, da wani mai haƙar ma’adanai da dai sauransu.

Sunayen waɗanda ake zargin sun hada da : Toheeb Albarka (malami); Lambe Kehinde da Lambe Taye; Francis Stephen; Olabode Yusuf, da Musbaudeen Akorede.

Sai kuma Moshood Okunola; Kayode Aderemi; Ayobami Olorunfemi; Paul Ayomide; Agboola Marvellous, da Adebisi Olatunde.

Sauran sun haɗa da Olaleye Solomon (mai haƙar ma’adanai); Akinade Samuel; Damilola Shagaya; Muhammed Awal; Adam Mubaraq; Ogundiran Nathaniel; Jamiu Ishola; Dauda Tunde; Abdullahi Sikiru; Kasali Adegoke; Jordan Adeyinka, da kuma direba, Ojeniyi Boluwatife.

Ragowar waɗanda ake zargi da damfanar sune, Adedamola Samson; Olarewaju Taofeek; Adewale Oloro, da Omogbolahan Ibrahim.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun su sun haɗa da motocin alfarma guda 10, kwamfutoci daban-daban, wayoyin hannu, firinta da dai sauran su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *