EFCC ta bukaci makarantar American International School Abuja da ta dawo $845,000, da Yahaya Bello ya tura musu

FB IMG 1714139416896

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta bukaci makarantar American International School, Abuja, da ta mayar da makudan kudi dala 845,000 da ake zargin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya biya dansa wanda dalibin babbar makaranta ne.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ola Olukoyede, a wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana yadda tsohon gwamnan da ke cikin rikici ya cire $720,000 daga asusun jihar domin biyan kudin makarantar yaronsa.

Ana zargin Bello ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da makarantar na biyan dala 845,000 har zuwa 2034 ga babban dansa mai suna Ali Bello.

Amma da aka gano laifin kudi da ake zargin tsohon gwamnan ya aikata tare da tsananta binciken hukumar EFCC, hukumar ta bukaci makarantar da ta dawo da kudaden nan take.

A martanin da makarantar ta mayar, ta amince da cewa Bello ya biya kudin ne a watan Satumbar 2021 kuma ya amince ta maido da kudaden da ya kai £760,000 bayan ta cire ayyukanta na ilimi da ake bawa dan tsohon gwamnan tun 2021.

Har ila yau makarantar ta makala rasiti da takardun yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a kan gudanarwar ta dan Bello.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan yarjejeniyoyi ita ce:

“Yarjejeniya tsakanin Malam Ali Bello da AISA na kudin makaranta kafin kammala karatu. Sharuɗɗa sun haɗa da biyan kuɗi, yuwuwar haɓaka kuɗi, da manufofin dawo da kuɗi. Mista Greg Hughes ne ya sanya hannu na AISA da Mista Ali Bello. Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da hakan.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *