Dubun Wasu Jami’an Ƴan Sanda Dake Da Hannu A Maguɗin Zaɓe Ta Cika

Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Rivers ta sanar da kama wasu jami’anta uku bayan da suka bayyana a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta wanda ya nuna suna da hannu a maguɗin zaɓe.

Bidiyon ya nuna jami’an ƴan sandan da ke bakin aiki a lokacin zaɓen cikin wata mota mai lamba “RRT O50”.

Sanarwar da kakakin rundunar, SP Garce Iringe-Koko ta fitar ta ce an kama motar domin gudanar da bincike.

Rundunar ta kuma bai wa al’ummar Rivers tabbacin ci gaba da aikinta na tabbatar da doka da oda da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda aka samu da aikata ba dai-dai ba.

Rundunar ta kuma buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu su kuma dakaci sanarwar sakamakon zaɓe a hukumance.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *