Jama’ar unguwar Sharada sun cafke wani matashi mai suna Jibrin Rimin kebe a Kano, a lokacin da yake kokarin satar Babur a bankin Union Bank dake Sharada a ranar Alhamis.
Alfijir Labarai ta rawaito matashin ya bayyana cewa abokinsa mai suna Sadik mazaunin Zoo road Kano ne ya koya masa sakar a mungun zare.
Sai dai ya ce idan saci Babur din suna kaiwa wani mai suna Haruna da akafi sani da Mallam Tijjani Kurna, inda yake siyan kowanne babur daya kan naira dubu tamanin ko dubu dari.
Wanda ake zargi ya kara da cewa, sun dade suna aikata wannan aika-aikar a sassan jahar Kano tsawon lokaci.
Tuni dai aka damka matashin a ofishin yan sanda na Sharada kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo