Dubun wani saurayi ta cika lokacin da yake lalata da Zakara turmi tabarya

IMG 20231208 145653

 Yan sanda a jihar Adamawa sun kama wani matashi dan shekara 17 mai suna Lawali Mori, mazaunin  Viniklang a karamar hukumar Girei, bisa laifin yin lalata da zakara.

Alfijir labarai ta rawaito dubun matashin dai ta cika ne biyo bayan korafin da wata mata Esther Dimas da ke zaune a Viniklang ta yi wa ‘yan sanda, bayan ta kama wanda ake zargi da aikata laifin.

 Lokacin da aka yi masa tambayoyi, Lawali wanda ake zargin ya kara bayyana cewa gaskiya ne yayi lalata da zakara,  amma bai iya bayar da dalilan da ya sa ya aikata haka ba.

 Da yake tabbatar da kamun, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sulaiman Nguroje, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, yayin da yake nuna damuwarsa, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.

Jaridar  Isyaku

IMG 20231207 WA0244 1
Alfijir Foundation

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *