Wani Mahaifin Da Ya Kai Wa ’Ya’yansa Cafka A Mama ya shiga hannun Jami an tsaro
Babbar Kotun Majistire a Jihar Lagos ta tsare wani mutum mai shekaru 45 a duniya da ake zargi da taba nonon ’ya’yansa mata biyu.
Jaridar Aminiya sun rawaito, mutumin da ake zargi ya fara yi wa kansa tsirara sannan ya rika kai ’ya’yan cafka a mama.
’Yan sanda sun ce lamarin mai cike da damuwa ta ban takaici ya faru ne a kan titin Sarumi da ke Unguwar Agege a Lagos.
Mutumin ya fara rufe da ‘ya’yansa a cikin daki sannan bayan ya cire kayan da ke, ya rika mulmula nonon ‘ya’yan nasa don ya motsa musu sha’awa su ba shi damar saduwa, a huce.
Bukatarsa bata kai ga biya ba yayan nasa suka kwarma ihu, har ya ankarar da wasu sojojin Har suka balle kofar dakin da karfin tsiya.
Magidanci da ake zargi da neman ya yi lalata da ‘ya’yansa ta hanyar taba musu nono bayan ya yi wa kansa tsirara da laifin ya tayar musu da sha’awa, a cewar jami’in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu. .
Jami’i mai shigar da kara, Supol Bisi Ogunleye ya ce “bayan an titsiya shi da kuma ya amsa laifinsa, an share da shi a gaban Kotun Majistare ta Ogba kan zargin aikata laifin cin zarafi.”
Mai sharia E. Kubeienje ta bada umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyara hali na Kiri kiri sannan ta dage karar zuwa ranar 25 ga watan Janairun 2022.