Kotu ta daure wani dan damfara na shekara guda bisa laifin N6m a Kano
Best Seller Channel
A ranar Litinin ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar wani Mai suna Daniel Uche Orji a gaban Mai Shari’a A.M Liman na Babban Kotun Tarayya da ke Kano a kan tuhume-tuhumen da aka yi masa na ci gaba da rike wasu kudade da aka yi masa.
Solacebase ta rawaito cewa an tafi da Daniel zuwa gidan yari ne biyo bayan bayanan sirri da ake zargin sa da aikatawa na zamba a intanet, ciki har da daukar matasa masu aikata laifuka ta yanar gizo.
Hukumar ta ce bayan samun Jami’an leken asirin, an kama wanda ake tuhuma a gidansa.
Fatan mu dai shine Allah ya cigaba da tona asirin bara gurbi a cikin wannan jahar tamu da Sauran duk kannin bata gari a kasar mu baki daya ameen.
Best Seller Channel