Dubun Wani Barawon Motar Asibiti Ya Sake Cika a Kano
JBest Seller Channel
Dubun wani mutum daya yayi awon gaba da motar asibiti daga jihar Kano ya nufi kasar Nijar da ita.
Kakakin Rundunar yan Sandan jihar Kano yayin holan ya bayyana barawon mai suna Saminu Sunusi dan shekaru 40 ya kware wajan dauke motocin mutane, wannan dai shine karo na 3 yana shiga hannun Jami an tsaro.
Best Seller Channel
Bayan shigarsa hannu a ranar Litinin ya ce, akwai abokin sa Mamuda da suke yin satar tare, kuma shine wanda ya kirawo shi wajan domin daukar wannan motar ma.
Kiyawa ya sake tambayarsa yanda ya fita a kotun a wancan Karon, ya ce ya amsa laifin sa, Alkali ya yanke mai hukunci aka karbi belin sa.
Dubun Saminu ta cika ne a Sai dai a iyakar Nigeria da Nijar a Babura ta jihar Jigawa, kuma ya karye a kafarsa garin gudu.