
Alfijr ta rawaito wasu da ake zargin jami’an hukumar ta DSS ne sun cafke babban jami’in tsaro na jihar, wasu kuma akan harin da aka kaiwa jami’in hukumar ta DSS, bisa zargin cin zarafin jami’an zabe da kuma wani babban jami’in tsaro.
Wasu gungun jama’a sun kutsa kai cikin otal din Green City da ke Yola tare da jan wasu jami’ai daga dakunansu biyo bayan ayyana ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin zababben gwamnan jihar da aka dakatar a yanzu.
Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna wani dattijo mai suna Farfesa Zuru, daya daga cikin kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) guda biyu da aka tura domin sa ido kan zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 15 ga Afrilu, yana wulakanta shi.

Babban hafsan gwamnan, Ahmad Umar, an ce shi ne da kansa ya ci zarafin babban jami’in da aka bayyana sunansa da Halilu wanda tuni ya isa otal a lokacin da babban jami’in ya iso tare da wasu ‘yan sanda da ke cikin gidan gwamnati da kuma wasu matasa kafin su yi masa bulala.
An yada hoton bidiyo na manyan jami’an da aka kaiwa hari sanye da yagaggun rigar kaftan da wasu da ba a san ko su waye ba ke yi musu tambayoyi a shafukan sada zumunta, lamarin da wasu da dama ke kallon abin kunya ga ‘yan sandan ta sirri.
Rundunar ta kuma kama akalla magoya bayan jam’iyyar PDP uku a wurare daban-daban a jihar bisa zargin hannu a hare-haren.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Barista Tahir Shehu, ya jagoranci wata zanga-zanga zuwa ofishin DSS da ke Yola a ranar Larabar da ta gabata don neman a sako mutanen uku “Mun zo da wannan ne domin mu yi rajistar zanzangar mu ta lumana tare da neman a gaggauta sakin ’yan jam’iyyarmu ba tare da wani sharadi ba, ana tsare da shi ba bisa ka’ida ba na kwanaki ba tare da an kai shi kotu ba, mun kuma kai wa Daraktan DSS na Jihar Adamawa da takardar neman izininsa ya ba wadanda ke tsare damar ganawa da lauyoyinsu da iyalansu domin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa ka tsare wani a kara fiye da sa’o’i 24 ba tare da kai shi kotu ba kuma ba tare da ba shi damar ganawa da danginsa ba,” in ji Shehu.
A halin da ake ciki, wata babbar kotu a karkashin mai shari’a Christopher Dominic Mapeo a ranar Alhamis ta bayar da umarnin tilastawa hukumar DSS ta saki mutanen uku ba tare da wani sharadi ba.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 3 ga Mayu, 2023.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ