
Alfijr ta rawaito cewa Damƙe Emefele na zuwa ne, awanni bayan da shugaban Kasa Bola Tinubu ya Sanar da dakatar da shi daga mukamin na Gwamna Bankin.
Rahotanni sun bayyana cewa Dakatar da tsohon gwamnan, nada Alaqa da binciken da ake gudanarwa akansa da ofishinsa.
Wannan yunkuri na Tinubu na daga cikin kudurorinsa, Wanda yake fatan cimma domin Samar da gyara a bangaren tattalin arzikin Najeriya.
Jami’an Tsaron na zargin gwamnan da tallafawa Yan ta’adda, sama da fadi da dukiyar alumma da sauran Badakala da dama.
DSS ta kama Emefele ne duk da cewa a baya, alkalin babbar kotun Tarayya dake Abuja Justice J.T Tsoho, yaki bayar da dama ga DSS domin ta kama Emefele.
Amma duk da wannan hani na kotu, bai yi tasiri kan jami’an ba, domin kuwa yanzu haka sun kama shi tare da sakaye shi a wajen su.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da gwamnan babban bankin Kasa CBN Godwin Emefiele daga mukaminsa.
Dakatarwar ta fara aiki ne nan take.
Daraktan yada labarai na osfishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’ar nan.
Ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa gwamnan na CBN ya biyo bayan wanu bincike da aka yi da kuma shirin yin garambawul a fannin hada-hadar kudi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ