
Alfijr ta rawaito hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta shaida wasu jiga-jigai a wata maƙarƙashiya da ake kitsawa don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar.
Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wadda wasu ke izawa ba kawai abu ne da ya saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kaucewa.
Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokraɗiyya da kuma zaman lafiyar al’ummar ƙasar.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.
Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga ‘yan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.
Ta dai ce masu kitsa makircin, a jerin tarukan da suke yi, suna auna batutuwa da dama a ciki har da yadda za su ɗauki nauyin zanga-zanga maras iyaka a manyan birane ta yadda daga bisani za a ayyana dokar ta-ɓaci.

Wani abin kuma shi ne, su samu umarnin kotu don hana rantsar da sabbin shugabanni da ƴan majalisa a matakin tarayya da jihohi.
‘Yan adawa a Najeriya sun soki lamirin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa wanda ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara a watan Fabrairun 2023. Sun yi zargin cewa zaɓen yana cike da kura-kurai, kuma an tafka maguɗi, baya ga amfani da tashe-tashen hankula don yin tarnaƙi ga zaɓen 25 ga watan Fabrairu.
Haka zalika, manyan ‘yan adawan da suka yi takara da Bola Ahmed Tinubu kamar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party duk sun shigar da ƙara a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe don ƙalubalantar nasarar Tinubu.

Ita dai Hukumar DSS ta bayyana goyon baya ga ƙudurin Shugaba Buhari na tabbatar da ganin an miƙa mulki ba tare da wani tashin hankali ba, kuma ta ce za ta yi aiki tuƙuru don ganin tabbatar hakan.
Ta kuma ce tana goyon bayan kwamitocin miƙa mulki da shugaban ƙasar ya kafa da kuma waɗanda aka kafa a jihohi.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
DSS ta kuma gargaɗi waɗanda ta kira masu shirin daƙile dimokraɗiyyar Najeriya su janye ƙudurinsu.
Ta kuma buƙaci hukumomi a ɓangaren shari’a da kafofin labarai da ƙungiyoyin farar hula su yi taka tsantsan don kada a yi amfani da su wajen tayar da fitina da ruguza zaman lafiyar ƙasar.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
I’m impressed with the news, and I’m supporting the DSS for there effort, thanks