Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano da ya yi takarar Gwamna a jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya biya wa ɗalibai Mata ƴan asalin jihar Kano 100 kuɗin Makaranta.
Alfijir Labarai ta rawaito cewa Dr. Gawuna ya tura wa Jami’ar Bayeron kuɗi har Naira Miliyan Sha Ɗaya domin biyan kudin.
Wani makusancin Dr. Gawuna ya tabbatar wa da Freedom Radio cewa jami’ar ta aike masa da sunayen ɗaliban da basu samu sun biya ba.
Idan za ku iya tunawa dai a kwanakin baya ne Gwamnatin Kano ta yi iƙrarin biya wa ɗalibai 7,000 ƴan asalin jihar kuɗin makarantar.
Shima Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Maliya ya biya yan kano ta arewa daliban B U K da kuma wadanda suke karatu a wajen kano yan yankin nasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb