Dattawan Arewa ga Tinubu: Ƴan Nijeriya ba za su iya biyan Naira miliyan 1,971,000 kuɗin wuta a shekara ba
Alfijir labarai ta rawaito kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a jiya ta bayyana damuwa da rashin jin dadi kan matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka na karin kudin wutar lantarki a kwanakin baya.
Ta kuma bayyana karin a matsayin “shirme” da kuma rashin mutunta walwala da jin dadin al’ummar Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, kungiyar ta arewa ta ce ta fahimci cewa wannan gagarumin karin kudin wutar lantarkin zai yi mummunan tasiri ga al’ummar da ke fama da matsala, wanda hakan zai kara girman gibin dake tsakanin masu arziki da talakawa.”
Ta ce karin farashin ya nuna wani babban nauyi da talakawan Najeriya za su fuskanta wajen samun wutar lantarki a kullum.
“A cikin sabon tsarin kudin wutan lantarki na sa’o’i 24 a kowace rana mutum zai kashe N5,400 mai ban mamaki, wanda adadin ya kai N162,000 da ba za a iya jurewa a kowane wata ba, sai kuma jimillar N1,971,000 mai ban mamaki a duk shekara.
“yan Nijeriya ba za su iya biyan wadannan makudan kudade ba, wadanda tuni ke fama da matsalar tattalin arziki da kuma kokarin samun biyan bukata.
“A yanzu dole ‘yan Najeriya su tashi su nemi hakkin su a wajen shugabanninsu, tare da tunatar da su cewa aikinsu na farko shi ne yi wa jama’a hidima, ba wai amfani da su don biyan bukatun kansu ba,” inji kungiyar.