Darajar Naira ta kara raguwa a kasuwar masu zuba jari da fitar da kayayyaki

Darajar Naira a jiya Litinin ta rabu da Dala a yayin da ake musayar ta a kan Naira dari 773.50 a fannin masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki.

Alfijir Labarai ta rawaito farashin Naira ya ragu da kashi 7.08 bisa dari a kan N736.62 da aka yi wa dala a ranar 8 ga watan Satumba.

Farashin ya rufe kan N771.49 zuwa Dala a jiya Litinin din.

Har sai da Dala ta kai N804.15 inda shine mafi girman farashin da aka samu a cinikin na jiya kafin ya daidaita akan N773.50.

Ana siyar da Naira a kan N722.39 ga Dala a kasuwar ranar.

An yi cinikin dala miliyan 37.86 a kasuwar masu zuba jari da masu fitar da kayayyaki a jiya Litinin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *