
Alfijr ta rawaito Jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun janye takardar da suka shigar na tilastawa hukumar zabe mai zaman kanta ta baiwa wakilansu damar shiga zaben. na tantance katunan zabe da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Atiku da PDP da ke kalubalantar sakamakon zaben da aka ayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress Bola Ahmed Tinubu, sun shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke zamanta a Abuja a ranar Laraba cewa sun janye maganar kararsu, basu da sha awa, yayin da aka bunciko karar mai lamba CA/PEC/10M/2023 domin saurare.
Atiku ta hannun tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Joe-Kyari Gadzama (SAN) ya shaidawa kotun cewa sun dakatar da kudirin su.

Wani dan kungiyar lauyoyin Atiku da ba ya so a ambaci sunansa ya ce, an shigar da karar ne saboda kalubale da kuma cikas da aka samu a ofishin INEC a lokacin da wakilan jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa suka je neman kayan zabe kamar yadda aka umarce su daga kotu,
Nigerian Tribune ta ruwaito. “Duk da haka, ranar 13 ga watan Maris, INEC da kanta ta kira kungiyar lauyoyin mu domin yin taro.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai