Alfijr ta rawaito Dan sanda ya kashe mace, sannan ya harbe kansa har lahira.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ilorin ta tabbatar da faruwar lamarin a Chapel Redemption, UMCA, unguwar Agba Dam da ke cikin babban birnin Ilorin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi ya fitar ta ce, “da misalin karfe 08:05 na ranar 2 ga Maris, 2023, bayanai sun isa ga rundunar ‘yan sandan, inda daga bisani wani mutum sanye da kakin ‘yan sanda mai suna Sajan. Olalere Michael “M,” ya harbe wata mace da ba a tantance ba, sannan ya harbe kansa ya mutu.

“Bayan bayanan da aka samu ga rundunar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, CP Paul Odama, psc, ya aike da tawagar ‘yan sanda da jami’an bincike zuwa wurin, inda aka zakulo gawarwakin aka ajiye a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin.

Binciken Likitoci ya tabbatar da cewa gawarwakin sun mutu”
“Rundunar ta bayyana a fili cewa lamarin ya faru ne sakamakon soyayyar da ta yi tsami tsakani, kuma ba shi da alaka da aikin ‘yan sanda”
“A halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan mummunan lamari, kuma za a bayyana rahoton binciken da zarar an kammala”.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇