Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Cikin kayayyakin da aka raba sun hada da injinan POS 50, na’urorin samar da wutar lantarki 120, da injin din dinki 120 da Kuma gadajen asibiti 200 sauran sun hada da teburan karatu a makaranta guda 800,
Alfijir Labarai ta rawaito ɗan majalisar wakilai mai wakiltar yankin Honorabul AbdulMalik Zubairu mai wakiltar mazabar Maru da Bungudu na jihar Zamfara a majalisar dokokin tarayya na jam’iyyar APC ya bayar da wannan Tallafin ne domin cikarsa kwanaki 100 Kan mukaminsa a majalisar tarayya Abuja.
An ba da kayayyakin ne a ranar Asabar da ya gabata, cikin kayayyakin da aka raba sun hada da injinan POS 50, na’urorin samar da wutar lantarki 120, da injin din dinki 120 da Kuma gadajen asibiti 200 sauran sun hada da teburan karatu a makaranta guda 800, baya ga gyara wasu asibitoci da kananan Asibitoci (Primary Head Center ) PHC, da makarantun Islamiyya da masallatai. .
Da yake jawabi a yayin bikin gudanar da rabon kyaututtukan dan majalisar tarayya, Honorabul Zubairu ya tabbatarwa al’ummar mazabarsa karin ribar romon dimukuradiyya , ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da zama nagari na wakilcin al’ummarsa a Majalisar Dokoki ta kasa domin al’ummarsa su ci gaba da cin gajiyar kuri’unsu a wannan zamani na dimokuradiyya.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar wadannan kyaututtuka da ayyukan da su yi amfani da su yadda ya kamata, domin a cewarsa, an yi su ne domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki, ya ce an samar da rijiyoyin burtsatse guda 45 tare da gina su domin samun saukin samun ruwan famfo a unguwanni 21 a mazabar Maru da Bungudu.
Ya ce ya kuma yi nasarar gudanar da aikin gyara da gina asibitoci da kuma samar da tallafin jinya ga dimbin al’ummar mazabar sa, ya kuma bayyana cewa ya bayar da taimako ga iyalan mutanen da ‘yan fashi suka kashe da Kuma jami’an tsaro da aka kashe a yankinsa a matsayinsa na dan majalisar tarayya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
MASHA’ALLAH ALLAH ALLAH YA KARA SHIGA LAMURAN SA,YA KUMA ZAMA ABIN MUSALI GA YAN MAJALISUN MU SUYI KOYI DA ABINDA YAYI NA ALKHAIRI ALLAH YASA HAKAN AMEEEEN