Dalilin Da Yasa Hukumar Kula Da Shari’a Ta Kano Ta Dakatar Da Alkalan Kotunan Majistiri A Jihar

FB IMG 1719309757358

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar kula da harkokin Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dakatar da alkalan Kotun Majistare uku saboda samun su da laifi a yayin gudanar da ayyukansu.

Alfijir labarai ta ruwaito kakakin kotunan jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya sanar cewa an dakatar da alkalai uku daga ayyukan shari’a, yayin da aka bayar da takardar gargadi ga magatakardar kotu guda daya.

Alkalan da aka dakatar sun hada da Talatu Makama ta kotun Majistare Mai lamba 29, da Babbar Majistire Rabi Abdulkadir ta Kotun Majistire mai lamba 48 da Alkalin kotun Majistire mai lamba 60, Tijjani Saleh Minjibir.

Na hudunsu shi ne Magatakarda Abdu Nasir da ke sashin daukaka kara da ke Babbar Kotun Jihar Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin karbar korafe-korafen jama’a na bangaren shari’ar ya sami Alkali Talatu Makama da laifin rashin da’a inda ta bayar da umarni ga Bankin GT ya tura kudi zuwa asusun mai shigar da kara bayan ta san cewa asusun a rufe yake, inda daga karshe aka sanya kudi cikin asusunta.

Haka kuma Hukumar ta same ta da laifin nuna rashin kwarewa inda taje karbar shari’a tare da bayar da oda ga ’yan sanda tun kafin shari’ar ta zo gabanta.

“Saboda haka an sauke Babbar Alkali Talatu Makama daga kujerarta an kuma dakatar da ita daga dukkan ayyukan shari’a nan take.

“Sai dai wannan bai shafi kasancewarta ma’aikaciyar gwamnati ba,” in ji sanarwar.

Takarda ta ci gaba da cewa, bayan binciken Hukumar ta JSC kan dambarwar shari’ar da ke tsakanin kwamishinan ’yan sanda da wani Abubakar Salisu da ke gaban Alkalin Kotun Majistare Mai lamba 48 Rabi Abdulkadir, an same ta da laifin yin sakaci a shari’a.

“Don haka hukumar ta dakatar da ita daga aikin shari’a na tsawon shekara guda.

“Sannan an umurce ta da ta daina duk wani aiki a Kotun Majistare mai lamba 48.”

Hukumar ta kuma dakatar da Alkalin Kotun Majistire mai lamba 60 Tijjani Saleh Minjibir na tsawon shekara 1 bisa samun sa da laifin rashin da’a.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *