Alfijr ta rawaito Gwamnatin Najeriya ta fayyace wasu dalilai hudu da suka sa ba za ta saurari batun kara wa’adin daina karbar tsoffin kudin naira ba a kasar.
Tabbas shugaba Buhari yana sauraron koke-koken al’umma kan wannan sauyi da matsin da suka shiga, kuma ana duba hanyoyin da ya kamata a bi domin saukaka wahalhalun talaka da kyautata musu. ta kuma kara da cewa ba wai saboda talaka ya shiga cikin matsi ba ne., sai dai sauyin a wannan lokaci ya zama wajibi ne. In Ji kakakin shugaban Mallam Garba Shehu.
Shehu ya ce abu na farko da ya kamata a sani shi ne ba wai an bijiro da wannan tsari ba ne saboda a galazawa mutane ko hanasu kasuwanci ko cigabansu ba, sai dai akwai bukatar a fahimci anyi hakan ne saboda masu sace dukiyar kasa da aikata rashawa.
Wawushe dukiyar kasa
Kuɗin Jabu
Rashawa da cin hanci
Ta’addanci
Gwamnatin Buhari ta ce ta fahimci akwai mutane da dama da suka wawushe dukiyar kasa ta haramtacciyar hanya, kuma wannan hanya ita ce daya tilo na karya su.
Gwamnati ta fahimci cewa kuɗin jabu ya yawaita a hannun jama’a, ana samun amsu buga irin wannan kuɗi a Najeriya, don haka canja takardar kudin zai daƙile wannan matsala.
Sannan akwai matsalar rashawa da cin hanci wanda ba bakon abu ba ne a Najeriya, mutane da dama na amfani da mukamansu wajen aikata rashawa.
Ta’addanci na daga cikin batutuwan da ke sake kassara wannan kasa, wanda ya ta’azzara matsalolin tsaro da batun sace mutane domin neman kuɗin fansa, da kuma daukar nauyin bata-gari da ‘yan bindiga. Don haka gwamnati na ganin sauya kudin kasar zai rife wannan kafa.
‘Bamu da niyar galazawa talaka’
Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya na sane da cewa ‘yan kasar da dama musamman kananan ‘yan kasuwa da ma’aikata da ɗaiɗaikun mutane kuɗi kawai suka sani su riƙe su yi cinikayya wasu ma ko hanyar banki ba su sani ba.
Don haka shugaban na tabbatar wa da ‘yan ƙasar cewa, ‘yan ƙasar ba su wahala ba, ta fuskar kasuwancinsu, da kuma samun tsaiko wajen canja tsoffin takardun kuɗinsu da sababbi a yayin da wa’adin da babban bankin ƙasar ya saka ke dab da cika.
Sannan daga lokacin da aka sanar da cewa za sauya kudi, an bada lokaci kusan kwanaki 100, don haka suma mutane sun ɗan yi sakancinsu, in ji shi
“A yan kwanakin nan babu abin da ba a gani ba, an gano kudade da dama da aka binne a karkashin kasa, wasu ma sun rube.
Shehu ya ƙara da cewa “An gano arzikin kasa da dama da aka boye wanda hakan ya taka rawa wajen gurgunta Najeriya”,
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
lokacin good luck ai bahaka yayiba tsakaninmu daku sedai Allah yasaka mana
Allah yakara daraja da daukaka
Kayi hakuri ka kyale jama,a wata shara,ar sai a lahira
Kayi hakuri ka kyale jama,a wata shara,ar sai a lahira
Ina murna da wannan hanyar sadarwar ta alfijir,
Muna godiya da kulawarku garemu