MU LEKA HUKUMAR CUSTOMS
FITOWA TA 11
Duk lokacin da wani kaya ya iso tashar jiragen ruwa ta Najeriya daga wata ƙasa, akwai matakai da dole ne a bi kafin a fitar da shi daga ƙarƙashin kulawar Hukumar Kwastam ta Najeriya (Nigeria Customs Service — NCS).
Daga cikin muhimman matakan akwai bayyana bayanan kaya, tantance nau’insu, ƙasar da suka fito, ƙimarsu da kuma harajin da ya dace a biya.
Wannan tsari yana da tasiri kai tsaye ga masu shigo da kaya, ‘yan kasuwa, kamfanonin jigilar kaya da kuma masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Sai dai akwai tambayoyi da ke buƙatar fahimta: Ta yaya Customs ke tantance ƙimar kaya? Shin dole ne ta karɓi farashin da ke kan invoice? Wane tsari ake bi wajen lissafa harajin shigo da kaya? Kuma mene ne haƙƙin ɗan kasuwa idan bai yarda da ƙimar da aka sanya wa kayansa ba?
Wannan shi ne abin da wannan fitowa ta bincika.
MENENE MA’ANAR ƘIMAR KAYAN DA AKE SHIGO DA SU?
Ƙimar kaya da Customs ke amfani da ita wajen lissafa harajin shigo da kaya ana kiranta Customs Value.
Ba wai kawai farashin da aka rubuta a invoice ba ne a kowane hali. Dokar Nigeria Customs Service Act, 2023, ta tanadi cewa ainihin farashin da aka biya ko wanda za a biya domin sayen kayan da aka sayar don shigo da su Najeriya shi ne tushen farko na tantance ƙimar kayan.
Sashe na 69(1) ya bayyana cewa Transaction Value shi ne babban tushen tantance ƙimar kaya.
Sashe na 69(2) kuma ya bayyana cewa wannan ƙima ita ce farashin da aka biya ko za a biya domin kayan, tare da gyare-gyaren da dokar ta tanada idan sun dace.
Sai dai akwai sharuɗɗan da dole ne cinikin ya cika kafin a yi amfani da wannan hanya. Daga cikinsu akwai cewa kada a samu wasu ƙuntatawa ko sharuddan ciniki da za su hana tantance ƙimar kayan yadda ya dace.
Wannan yana nufin cewa Customs ba ta da damar watsi da farashin ciniki kawai ba tare da dalili da bin tsarin da doka ta tanada ba. Haka kuma, ba dole ba ne ta karɓi duk farashin invoice kai tsaye idan akwai dalilan da suka sa ba za a iya amfani da wannan farashi a matsayin Transaction Value ba bisa sharuɗɗan dokar.
SHIN CUSTOMS ZA TA IYA ƘARA WASU KUƊAƊE A KAN FARASHIN INVOICE?
Eh, a wasu yanayi.
Sashe na 69(10) na dokar 2023 ya tanadi wasu kuɗaɗe da za a iya ƙarawa cikin farashin ciniki idan ba a riga an haɗa su cikin farashin da aka biya ko za a biya ba.
Daga cikin su akwai:
– Kuɗin kwamitin dillanci ko tallace-tallace a wasu yanayi.
– Kuɗin kwantena da marufi.
– Wasu kayayyaki ko ayyukan da mai saye ya samar domin samar da kayan da aka shigo da su.
– Wasu kuɗaɗen lasisi ko royalties da suke da alaƙa da kayan.
– Kuɗin jigilar kaya zuwa tashar ko wurin shigar da su Najeriya.
– Kuɗin lodawa, sauke kaya da kula da su yayin jigila.
– Kuɗin inshorar kayan.
Sai dai dokar ta tanadi cewa duk wani ƙari ga farashin da aka biya ko za a biya dole ne ya kasance bisa sahihan bayanai masu iya ƙididdigewa.
Haka kuma, ba za a ƙara wasu kuɗaɗe ba sai waɗanda dokar ta tanada.
IDAN CUSTOMS BA TA YARDA DA FARASHIN INVOICE BA, ME TAKE YI?
Sashe na 77 na Nigeria Customs Service Act, 2023, ya bai wa Hukumar damar bincika sahihanci da daidaiton duk wata sanarwa, takarda ko bayani da aka gabatar domin tantance ƙimar kaya.
Wannan yana nufin cewa idan Customs ta samu dalilin shakkar farashin da aka bayyana, tana da damar neman ƙarin bayani ko takardun da za su tabbatar da sahihancin farashin.
Sai dai idan ba za a iya amfani da Transaction Value ba bisa sharuɗɗan dokar, akwai wasu hanyoyin tantance ƙimar kayan da dole ne a bi bisa tsarin da dokar ta tanada.
HANYOYI SHIDA DA DOKA TA TANADA WAJEN TANTANCE ƘIMAR KAYA
Nigeria Customs Service Act, 2023, ta tanadi hanyoyi shida na tantance ƙimar kayan da aka shigo da su Najeriya.
1. Transaction Value — Sashe na 69
Wannan ita ce hanyar farko da doka ta tanada. Ana duba ainihin farashin da aka biya ko za a biya domin kayan, tare da ƙarin kuɗaɗen da dokar ta tanada idan sun dace kuma ba a riga an haɗa su cikin farashin ba.
2. Identical Goods — Sashe na 70
Idan ba za a iya tantance ƙimar kaya ta hanyar Transaction Value ba, za a iya amfani da farashin irin waɗannan kaya da suka yi daidai da kayan da ake tantancewa, waɗanda aka sayar don shigo da su Najeriya a kusan lokaci ɗaya.
3. Similar Goods — Sashe na 71
Idan ba a samu damar amfani da hanyoyin da suka gabata ba, doka ta tanadi amfani da farashin kaya masu kama da juna ta fuskar halaye, inganci da amfani.
4. Deductive Value — Sashe na 72
A wannan hanya, ana amfani da farashin da aka sayar da kayan ko makamantansu a Najeriya, sannan a cire wasu kuɗaɗe da dokar ta lissafa, kamar ribar dillali, kuɗin cikin gida da harajin da ya dace.
5. Computed Value — Sashe na 73
Wannan hanya tana dogara ne da ƙididdigar kuɗin da aka kashe wajen samar da kayan, ciki har da kuɗin kayan da aka yi amfani da su, kuɗin sarrafawa da wasu kuɗaɗen riba da gudanarwa.
6. Residual Value — Sashe na 74
Idan ba za a iya tantance ƙimar kaya ta sauran hanyoyin da aka ambata ba, doka ta tanadi amfani da wasu hanyoyin da suka dace da ƙa’idojin yarjejeniyar ƙasa da ƙasa, bisa bayanan da ake da su a Najeriya.
Akwai wani muhimmin batu game da tsarin amfani da waɗannan hanyoyi. Sashe na 72(1) ya tanadi cewa idan ba za a iya amfani da hanyar da Sashe na 69 da 70 suka tanada ba, za a yi amfani da hanyar da Sashe na 72 ya tanada, ko kuma Sashe na 74 idan hakan bai yiwu ba. Haka kuma, sashe ya tanadi yiwuwar sauya tsarin amfani da hanyoyin da aka ambata a Sashe na 72 da 74 idan mai shigo da kaya ya buƙata.
Sai dai jagorar tantance ƙimar kaya da Hukumar Customs ta wallafa ta bayyana wannan batu da wata hanya dabam, inda ta danganta sauya tsarin da hanyoyin Deductive Value da Computed Value.
Wannan bambanci tsakanin lafazin dokar da jagorar Hukumar yana buƙatar ƙarin bayani daga Customs domin a fahimci yadda take aiwatar da tanadin.
Haka kuma, Sashe na 74(2) ya hana amfani da ƙimar da aka ƙirƙira ko ƙimar da ba ta da ingantaccen tushe. Daga cikin hanyoyin da dokar ta hana akwai amfani da mafi girman ƙimomi biyu a matsayin ƙimar Customs, amfani da mafi ƙarancin ƙimar Customs da kuma wasu ƙimomi na zato ko ƙimomin da ba su da tushe.
Wani muhimmin haƙƙi kuma shi ne cewa Sashe na 74(3) ya tanadi damar mai kaya na neman a sanar da shi a rubuce ƙimar da aka tantance da kuma hanyar da aka yi amfani da ita wajen tantance ta, musamman idan an yi amfani da hanyar Residual Value.
YAYA AKE TANTANCE HARAJIN SHIGO DA KAYA?
Bayan tantance ƙimar kaya, ana buƙatar sanin nau’in kayan da kuma ƙasar da suka fito domin tantance harajin da ya dace.
A nan ne Harmonised System (HS) Code da ECOWAS Common External Tariff (CET) suke da muhimmanci.
HS Code yana taimakawa wajen tantance nau’in kaya da rukunin da suka shiga. Wannan rukunin yana taimakawa wajen gano jadawalin harajin da doka ta tanada.
Ƙasar asalin kaya ma tana da muhimmanci saboda wasu kayayyaki na iya samun rangwamen haraji bisa yarjejeniyar kasuwanci da ta shafi ƙasashen da suka fito.
Saboda haka, ba daidai ba ne a ce duk kayayyakin da aka shigo da su Najeriya suna biyan kaso ɗaya na haraji.
Harajin da za a biya yana danganta da nau’in kayan, HS Code, ƙasar asalin kaya, ƙimar Customs da kuma dokokin haraji da ke aiki a lokacin shigo da kayan.
Ya kamata kuma a bambanta tsakanin Customs Value da Import Duty. Customs Value ita ce ƙimar da ake amfani da ita wajen lissafi, yayin da Import Duty shi ne harajin shigo da kaya da ake biya bisa ƙa’idar da ta shafi kayan.
Haka kuma, akwai wasu kuɗaɗen hidimomin tashar jiragen ruwa ko wasu kuɗaɗen da za a iya biya daban, waɗanda ba harajin Customs ba ne kai tsaye. Ya kamata a bambanta su domin mai shigo da kaya ya fahimci abin da kowanne kuɗi yake wakilta.
SHIN DOKA TA BAI WA ƊAN KASUWA DAMAR ƘIN AMINCEWA DA ƘIMAR CUSTOMS?
Eh.
Sashe na 269 na Nigeria Customs Service Act, 2023, ya bai wa mutumin da hukuncin Customs ya shafa damar neman a ba shi dalilan hukuncin a rubuce.
Haka kuma, Sashe na 269(2) ya bai wa mutum damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin Customs da ya shafi:
– Tantance nau’in kaya (classification).
– Tantance ƙimar kaya (valuation).
– Tantance ƙasar asalin kaya (origin).
– Sauran matakan Customs da suka shafe shi kai tsaye.
Sashe na 269(3) ya tanadi cewa dole ne a gabatar da ƙorafin a rubuce, tare da dalilan ƙorafin da hujjojin da ke goyon bayansa, cikin kwanaki 30 daga ranar hukuncin ko gazawar da ake ƙorafi a kanta.
WANE TSARI AKE BI WAJEN ƊAUKAKA ƘARA?
Sashe na 270 na dokar 2023 ya tanadi matakai na ɗaukaka ƙara kamar haka:
1. Da farko, a gabatar da ƙorafi ga sashen Customs da ya yanke hukuncin, wanda zai bayar da amsa a rubuce cikin kwanaki 21 na aiki.
2. Idan mai ƙorafi bai gamsu da hukuncin ba, zai iya ɗaukaka ƙara ga Comptroller-General cikin kwanaki 30.
3. Idan har yanzu bai gamsu ba, zai iya neman a miƙa batun ga World Customs Organization (WCO).
4. Idan bai gamsu da hukuncin Comptroller-General ba, yana da damar kai ƙarar gaban kotun da ta dace.
Wannan yana nuna cewa mai shigo da kaya ba shi da zaɓi guda ɗaya kawai idan ya samu saɓani da Customs kan ƙimar kayan da aka shigo da su.
SHIN ZA A IYA RIƘE KAYA YAYIN DA AKE ƊAUKAKA ƘARA?
Sashe na 271 ya tanadi cewa gabatar da ƙorafi ba ya dakatar da aiwatar da hukuncin Customs kai tsaye.
Sai dai Sashe na 271(2) ya tanadi yanayin da za a dakatar da aiwatar da hukuncin yayin da ake sauraron ƙorafi. Daga cikin abubuwan da ake buƙatar la’akari da su akwai ko hukuncin ya saɓa wa dokokin Customs da ke aiki, da kuma yiwuwar samun babbar illa da ba za a iya gyarawa cikin sauƙi ba ga abin da ake ƙara a kai ko mutumin da abin ya shafa.
Haka kuma, Sashe na 75 ya tanadi cewa idan Customs ta buƙaci ƙarin lokaci domin kammala tantance ƙimar kaya, za a iya ba mai kaya damar karɓar kayan daga ƙarƙashin kulawar Customs idan ya samar da isasshen guarantee ko security da zai tabbatar da biyan kuɗaɗen da za a iya binsa.
Wannan tanadi yana da muhimmanci wajen rage yiwuwar jinkirin fitar da kaya yayin da ake kammala tantance ƙimarsu.
ME YA SA WANNAN BAYANI YAKE DA MUHIMMANCI GA ‘YAN KASUWA?
Idan mai shigo da kaya bai fahimci yadda ake tantance ƙimar kaya da lissafin haraji ba, zai iya fuskantar matsaloli wajen tsara kuɗaɗen kasuwancinsa.
Haka kuma, rashin fahimtar bambanci tsakanin Customs Value, HS Code, Import Duty da sauran kuɗaɗen hidimomin tashar jiragen ruwa na iya jawo rikice-rikice tsakanin masu shigo da kaya da hukumomin da abin ya shafa.
Saboda haka, yana da muhimmanci mai shigo da kaya ya riƙa adana invoice, takardun saye, packing list, takardun jigila, inshora da sauran bayanan da za su taimaka wajen tabbatar da ainihin cinikin da aka yi.
Haka kuma, ya kamata ya nemi bayanin dalilin duk wani sauyi da aka yi wa ƙimar kayan da ya bayyana, da kuma yadda aka lissafa kuɗin da aka ɗora masa, maimakon ya tsaya ga karɓar ƙarin kuɗi ba tare da fahimtar tushensa ba.
TAMBAYOYIN DA ALFIJIR LABARAI KE SON HUKUMAR CUSTOMS TA AMSA
A wannan bincike, Alfijir Labarai na neman ƙarin bayani daga Hukumar Customs kan waɗannan tambayoyi:
1. Wane tsari ne Hukumar ke amfani da shi wajen tantance sahihancin farashin da masu shigo da kaya suka bayyana a invoice?
2. Kayayyaki nawa ne aka yi wa ƙarin ƙima ko gyaran valuation saboda bambanci tsakanin farashin da aka bayyana da wanda Customs ta tantance a shekarar 2025 da kuma shekarar 2026 zuwa yanzu?
3. Ta yaya Hukumar ke tabbatar da cewa jami’ai suna bin hanyoyin tantance ƙimar kaya da Sashe na 69 zuwa 74 na Nigeria Customs Service Act, 2023, ya tanada?
4. Shin Customs tana da tsarin da mai shigo da kaya zai iya amfani da shi wajen ganin yadda aka lissafa ƙimar kayansa da harajin da aka ɗora masa?
5. Ƙorafe-ƙorafe nawa ne da suka shafi valuation da classification Hukumar ta samu a shekarar 2025 da kuma shekarar 2026 zuwa yanzu, kuma nawa aka warware?
6. Ta yaya Hukumar ke tabbatar da cewa masu shigo da kaya suna samun cikakken bayanin dalilin duk wani ƙarin ƙima ko haraji da aka ɗora musu?
7. Shin Hukumar tana da tsarin da mai shigo da kaya zai iya amfani da shi wajen samun cikakken bayani a rubuce kan ƙimar da aka sanya wa kayansa da hanyar da aka bi wajen tantance wannan ƙima, kamar yadda Sashe na 74(3) na dokar 2023 ya tanada?
8. Sashe na 72(1) na Nigeria Customs Service Act, 2023, ya bayyana sauya tsarin amfani da hanyoyin da ke ƙarƙashin Sashe na 72 da 74, amma jagorar Customs kan valuation ta danganta wannan sauyi da Deductive Value da Computed Value. Wane bayani ne Hukumar za ta bayar kan wannan bambanci, kuma wane tsari ne jami’anta ke bi a aikace?
KAMMALAWA
Tantance ƙimar kayan da ake shigo da su da lissafin harajin Customs muhimmin ɓangare ne na tsarin kasuwancin ƙasa da ƙasa.
Dokar Nigeria Customs Service Act, 2023, ta tanadi hanyoyin tantance ƙimar kaya, ta bai wa Customs damar binciken sahihancin takardun da aka gabatar, sannan ta bai wa masu shigo da kaya damar ɗaukaka ƙara idan ba su gamsu da hukuncin da aka yanke musu ba.
Saboda haka, gaskiyar lissafi, bayyana dalilan tantance ƙima da bin tsarin doka suna da muhimmanci wajen tabbatar da amincewa tsakanin Customs da ‘yan kasuwa.
Alfijir Labarai na kira ga Hukumar Customs da ta ƙara samar da bayanai masu sauƙin fahimta game da tsarin tantance ƙimar kaya, lissafin haraji da hanyoyin da ‘yan kasuwa za su bi idan sun samu saɓani da Hukumar.
Za mu ci gaba da binciken wannan batu, tare da gabatar da martanin Hukumar idan ta amsa tambayoyin da muka aika mata.
MU BINCIKA. MU TAMBAYA. MU BAYYANA ABIN DA DOKA TA CE.
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
