Da Ɗumi Ɗuminsa: Gwamnatin Kano Ta Kwato Motocin Kwashe Shara 13 Da Suka Bata


Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado ta kwato wasu motocin kwashe shara guda goma 12, mallakin gwamnatin jiha.

Alfijir Labarai ta rawaito Motocin wadanda yanzu haka suna cikin hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano, wadanda motocin mallakin hukumar kwashe shara ta jihar kano ne.

Yayin da ya ziyarci hukumar domin ganewa idanunsa motocin da aka kwato, kwamishinan harkokin Sufuri da gida na jihar kano, Engr. Muhammad Diggwal yace motocin an rasa su ne tun a gwamnatin data gabata, wanda hakan tasa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin nemo su duk Inda suke.

Yanzu haka wadannan Motocin da  hukumar ta kwato su ne daya bayan daya, wasu su daga cikinsu ma an fara sauya musu fasali, cikin su har da katafila guda daya,

Kwamishinan ya ce babu shakka wannan Abu da akai an yi abun daya dace, kuma zamu tabbatar al’ummar jihar kano sun cigaba da morarsu”.

Ya kara da cewa zasu jira hukumar ta kammala bincike akan yadda aka motocin suka bace, sannan sai hukumar ta ɗauki matakin da ya dace akan Wanda aka samu da laifi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

One Reply to “Da Ɗumi Ɗuminsa: Gwamnatin Kano Ta Kwato Motocin Kwashe Shara 13 Da Suka Bata”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *