Da Yiwuwar Alhazan Nijeriya Su Biya Naira miliyan 3.3 kuɗin Hajjin Bana

Harami

Alfijr ta rawaito ranar Juma’a ne a ke sa ran Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, za ta sanar da tabbataccen kuɗin aikin Hajjin bana.

Wata majiya mai karfi a NAHCON ta shaidawa Hajj Reporters cewa hukumar na shiri na karshe wajen sanar da kudin aikin Hajjin na bana.

Sai dai kuma majiyar ta tabbatarwa Hajj Reporters cewa in dai ba wani canji na gaggawa aka samu ba, farashin aiki Hajjin bana zai kai Naira miliyan 3.3.

Ma’ajiyar ta ce tsadar kayayyaki da hauhawar farashi na ayyuka a Saudiya ne ya haifar da tashin farashin aikin Hajjin.

Majiyar ta kara da cewa, ” a bara, kuɗin kama masauki da Riyal 2000 ne amma ana kuɗin ya nuna sau biyu.

“A halin yanzu haka ma wasu jihohi ma Nijeriya na fama da wahalar samun masaukai a kusa da masallacin harami,” in ji majiyoyin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *