Da Dumi Duminsa: DSS ta kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai a Kano

FB IMG 1781282541802

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani mutum mai shekara 30 da haihuwa, Muhammad Abubakar, bisa zargin safarar makamai a Jihar Kano.

DSS ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Gezawa bayan samun bayanan sirri, yayin da yake kokarin kai bututun makamin roka guda huɗu (RPG), bindigogi kirar AK-47 guda uku da bindigu biyu marasa harsasai zuwa Funtua a Jihar Katsina.

A cewar hukumar, wanda ake zargin direban sufuri ne, kuma ya amsa cewa ya karɓi makaman daga wani mutum mai suna Bello a yankin Maigatari da ke kan iyakar Jihar Jigawa domin kai su wani yankin da matsalar tsaro ta yi kamari.

Muhammad Abubakar ya ce an yi masa alkawarin biyan sa Naira 450,000 bayan ya isar da kayan, amma jami’an tsaro suka kama shi kafin ya kai ga kammala aikin.

DSS ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da take ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *