DA DUMI-DUMI: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Harbin Kan Mai Uwa Da Wabi A Zone one Shiyyar Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne sun yi harbin kan mai uwa da wabi a hedikwatar ‘yan sanda ta Zone 1 da ke kan titin BUK a Kano.

A cewar majiyoyin tsaro, ‘yan ta’addan sun zo ne a cikin motoci uku da misalin karfe 12:30 na ranar Juma’a

Majiyar ta ce ana kara karfafa tsaro a kewayen hedikwatar domin dakile yiwuwar kai hare-hare daga ‘yan ta’addar.

Alfijr

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan ta’addan sun kai hari a hedikwatar ne a lokacin harin na ranar 20 ga watan Janairun 2012, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 185 a jihar.

Cikakkun bayanai na nan tafe kamar yadda Jafar Jafar ya rawaito