Mahaifiyar ‘yar majalisar dokokin Kano da aka sace ta samu ‘yanci bayan an biya kudin fansa
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Mahaifiyar ‘yar majalisar dokokin Kano da aka sace, Hajiya Zainab, ta samu ‘yanci bayan an biya ta kudin fansa.
Solacebase ta ruwaito, an sace Hajiya Zainab, mahaifiyar Isiyaku Ali Danja, shugaban marasa rinjaye, majalisar dokokin jihar Kano a ranar 12 ga watan Janairu, 2021. , Mahaifiyarsa ta samu ‘yanci bayan an biya shi N40m.
Ali Danja wanda shi ne kakakin majalisar ya ce suna kan hanyarsu ta dauko ta ne daga wata karamar hukuma da ke jihar Jigawa inda masu garkuwa da mutane suka ajiye ta.