Da Dumi-Ɗuminsa: Fashewar Wani Abu Ta Kashe Mutune 3, A Zuwan Shugaba Buhari jihar Kogi

Alfijr ta rawaito Rahotanni daga jihar Kogi na nuna cewa an samu fashewar wani abu tare da kashe mutane uku a Okene, a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara.

A yayin ziyarar shugaba Buhari na nufin kaddamar da ayyukan da gwamna Yahaya Bello ya aiwatar a sassan jihar.

Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito, a fadar Oyinoyi da ke karamar hukumar Okene, a yankin Arewa ta tsakiya, wato mahaifar gwamna jihar.

Sai dai jami’an tsaro sun isa wurin, har kuma ya zuwa yanzu dai gwamnatin jihar ba ta ce uffan ba kan faruwar lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *