Ya kuma nada sabbin mataimakan gwamnoni hudu da suka hada da Emem Nnana Usoro da Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Philip Ikeazor da kuma Bala M. Bello.
Alfijir Labarai ta rawaito Chief Ajuri Ngelale mai bawa shugaban kasa shawara na musamman ya bayya cewar, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar
Wannan umarni ya yi daidai da sashe na 8 (1) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007, wanda ya baiwa shugaban tarayyar Najeriya ikon nada gwamna da mataimakan gwamnoni hudu (4) a babban bankin kasar. na Najeriya (CBN).
Bugu da kari kuma, shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mataimakan gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar (5) a matakin farko, har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da su, kamar yadda ta lissafo a kasa:
(1) Mrs. Emem Nnana Usoro
(2) Malam Muhammad Sani Abdullahi Dattijo
(3) Malam Philip Ikeazor
(4) Dr. Bala M. Bello
Shugaba Bola Tinubu na sa ran wadanda aka zaba a sama za su samu nasarar aiwatar da muhimman sauye-sauye a babban bankin Najeriya, wanda zai kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya da abokan huldar kasa da kasa wajen sake fasalin tattalin arzikin Najeriya don samun ci gaba mai dorewa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@musa_bestseller
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb